Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun yi garkuwa da matar dan majalisar dokokin jihar Zamfara, Aminu Ardo Jangebe tare da ‘ya’yan hudu.
An kuma bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi awon gaba da wasu makusantan sa biyu, Alhaji Yahaya da Sa’adu Mainama.
Wani mazaunin unguwar, Sani Abubakar, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun isa garin ne da misalin karfe 11 na daren ranar Alhamis inda suka fara harbe-harbe a kaikaice don tsoratar da mutane.
Jama’a da dama sun gudu da jin karar harbe-harbe, a cewar Abubakar, yayin da wasu kuma suka rufe kofofinsu don gudun kada a sace su.
Ya yi ikirarin cewa ‘yan bindigar sun je gidan Aminu Ardo ne suka fasa kofar don shiga.
Ya ce, “Nan take ‘yan fashin suka shiga gidan, suka yi awon gaba da matar Honourable da ‘ya’yansa hudu.
“A yayin da suke fitowa daga gidan, sai suka hango wasu makwabtansa guda biyu, MalamYahaya da Sa,adu Mainama wadanda suma suka yi awon gaba da su.
”A cewar Abubakar, ‘yan ta’addan sun kuma sace babur din daya daga cikin mutanen da aka sace.
Yunkurin jin ta bakin dan majalisar ya ci tura domin bai amsa wasu kiraye-kirayen da aka yi wa wayarsa ba.
Alhaji Ibrahim Dosara, kwamishinan yada labarai na jihar, shi ma bai dauki wayarsa ba, duk da ya tabbatar wa Jaridar BBC hausa faruwar lamarin.
Da aka tuntube don jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Mohammed Shehu, ya ce “zai sanar da karin bayani”.
Amma, Shehu bai mayar da martani ba har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.