Yadda yan ta’adda suka sace mazan wani kauye a jihar Zamfara


Wasu yan bindiga da ake zaton masu yin garkuwa da mutane ne sun shiga wani kauyen Randa na karamar Hukumar Maru a Jihar Zamfara sun sace mazajen garin. 


A yayin harin mutane 20 ne suka rasa ransu, an ce sun shiga kauyen ne a sakamakon bindigoginsu da aka sace musu wanda suke zargin yan kauyen. 


Rahotonni sun tabbatar cewa Lawali Damina gawartaccen dan bindiga da ya addabi kauyukan jihar Zamfara shine ya jagoranci kai hari a kauyen Randa cikin mazan da aka dauke har da wasu kwanan yara. 


Shafin RFI Hausa ya rawaito cewa tawagar Damina sun yi fada ne da wasu abokan gabarsu akan wata budurwa wanda ya kai ga an rasa bindiga guda biyu inda suka yi zargin yan kauyen Randa ne suka sace. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post