Yadda sojoji suka yi luguden wuta ga yan ta’addan Boko Haram


A wani mummunan farmaki da rundunar sojin Najeriya suka kai a maboyar 'yan Boko Haram dake jihar Borno sun yi nasarar kashe mayakan da dama. 


Dakarun Operation Hadin Kai sune suka kai harin a wani yanki dake kan hanyar Wajiroko zuwa Damboa, wanda ya zarce zuwa Maiduguri, inji wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta. 


A lokacin harin, sanarwar ta ce an hallaka mayaƙan ƙungiyar Boko Haram da na ISWAP da dama. Haka nan dakarun sun ƙwato bindigogi da harsasai, da motoci da kuma kayan yaƙi da dama.


Ko a satin da ya gabata sai da aka samu irin wannan nasarar inda sojojin suka kashe da yawa daga cikin mayakan na Boko Haram. Wannan yana nuna babbar nasara a ci gaba da yaki da ake yi da yan tayar da kayar baya. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post