Yadda Fashewar tukunyar gas ta kashe mutum 5 da jikkata 40 a wajen shagalin aure - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Yadda Fashewar tukunyar gas ta kashe mutum 5 da jikkata 40 a wajen shagalin aure



Yan sanda a ranar Juma'a sun ba da rahoton cewa mutane biyar ne suka mutu sannan wasu fiye da 40 suka jikkata bayan fashewar wata tukunyar iskar gas din girki a wajen wani bikin aure a Indiya. 


Jami'in Æ´an sanda, Anil Kayal ya ce fashewar ta faru ne a wani kauye da ke Rajasthan lokacin da bakin daurin auren ke taruwa don cin abincin biki.


Kayal ya kara da cewa fashewar ta ruguza wani É“angare na gidan da ke gundumar Jodhpur.


A cewar binciken farko da ‘yan sanda suka yi, tukunyar iskar gas din na cikin wani dakin ajiya ne, ya zubo, ta kama wuta kuma ta fashe. Mutane hudu ne suka mutu nan take yayin da daya ya rasu a asibiti.


Kayal ya ce adadin na iya ƙaruwa yayin da wasu da dama da abin ya shafa su ka samu ƙoƙƙkone, wasu kuma yanayin da su ke ciki ya yi tsanani.

Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel