Wata mata da ake zarginta da kashe dan cikin ta dan watanni 11 da haihuwa a kauyen Ugep, da ke karamar hukumar Yakurr na jihar Cross River.
Shafin Jaridar BBC sun rawaito cewa yan sanda sun yi nasarar kame wacce ake zargi a lokacin da matasan unguwar ke kokarin yi mata duka.
Lokacin da ya tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar 'yan sanda a jihar, SP Irene Ugbo ya ce yanzu haka matar tana hannun hukuma.
Ugbo ya kara da cewa "ana ci gaba da bincike domin gano dalilin da ya sa ta yanka yaron, amma labarin da muka samu shi ne tana da tabin hankali."
Labarin dai ya dauki hankalin jama'a sosai musamman a kafafen sada zumunta inda ake ta samun bambancin ra'ayi.