Allah Ya albarkace mu da mata masu yin abin ban mamaki" - Wani dan Najeriya ya rubuta a lokacin da yake baje kolin kayan abinci da matarsa ta saya masa don bikin Kirsimeti
Mutumin a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter ya bayyana yadda yai mamaki ga irin kyautar ban mamaki da matar ta yi masa.
Ina zaune a parlour ina kallon tv, sai naji karar babur jikin gidan mu, raina yana tunanin sun kawo siminti ne ga mai gidana da yake gina gida. Abu na gaba sai na ji muryar matata, tana kirana, a cewar sa.
Bayin Allah!! Na sauka kasa, na tarar da matar ta siya min kayan kirsimeti.
Bayan wallafa hoton kyautar da ya samu daga wajen matarsa mutane da dama sun yi tsokaci inda suke taya shi murna da godiya ga matarsa kan abinda ta yi.
Wasu kuwa na cewa ya yi sa'ar mace domin ba kasafai ake samun mata na yiwa mijin su ko saurayin su kyuta ba.