Mustapha Umar ya koka kan Yadda ya tsinci kansa a wani mawuyacin hali bayan da amaryarsa ta haihu watanni uku da yin auren su.
A wata tattaunawa da yai da shafin Aminiya, Mustapha ya bayyana kaduwarsa da mamakin haihuwar amaryarsa a cikin watanni 3 da kwanaki 14.
Yace bai taba tunanin cewa amaryarsa za ta yaudareshi ba. Haihuwar da ta yi ya jawo cece-Kuce a gidan mu, wanda hakan yasa kowa yasa halin da ake ciki.
Ya kara da cewa shi ba su taba aikata fasikanci ba kafin su yi aure balle yai tunanin cewa cikin nasa ne ba. Wanda tun bayan haihuwarta auren namu yazo karshe.
A ra'ayin da jama'a suke bayyanawa wata uwa mai suna Maryam Jibrin Kofar Bai ta bayyana hakan a matsayin matsala wacce ta zama ruwan dare a cikin al'umma.
Ta bayyana faruwar hakan a matsayin sakacin iyaye da kuma rashin kamun kai daga wajen yarinya wanda yake haddasa yawan faruwar hakan.
Ta Kara da cewa iyayen yarinya suna sani Idan yarsu ta yi ciki amma saboda son zuciya sai su rufe abin, wasu kuma har bin bokaye suke yi don a kwantar da cikin har sai bayan ta yi aure.
A karshe ta yi Kira da iyaye da su kara saka ido sosai akan zirga-zirgar ya’yansu da irin kawayene da suke yin mu'amala.