Kotun Majistare dake zamanta a birnin Zariya dake jihar Kaduna ta tsare wani matashi kan zargin dabawa mahaifinsa wuka a lokacin da yake Sallah a masallaci.
Shafin Aminiya ya rawaito cewa matashin da ake zargi dan shekaru 21 ana tuhumar sa da yunkurin kashe mahaifin sa a lokacin da yake yin sallah a wani masallaci dake unguwar Rimin Tsiwa a birnin Zariya.
A Zaman Kotun an nemi alkali Ramatu Dalhatu ta bayar da belin matashin sai dai ta ki amincewa ta bayar da belinsa inda tace a saka shi a kurkuku har zuwa lokacin da ma'aikatar shari'a ta Jihar Kaduna ta yanke shawara akan lamarin.
ALLAH YA KARE MU DAGA SHARRIN WAN NAN ZAMANI.
ReplyDelete