Kasurgumin Dan Bindiga Da Ya Addabi Kauyukan Kaduna Ya Shiga Hannun Hukuma



Hukumar yan sandan jihar Kaduna ta yi nasarar kame kasurgumin Dan Bindiga da ya addabi Kauyukan jihar. 


Shi dai dai Dan Bindiga ana zarginsa da dillancin harsasai da bindigogi a Zaria. Kakakin rundunar yan sandan jihar Jalige shine ya bayyana yadda suka yi nasarar kama shi a ranar Lahadi. 


Ya kara da cewa sun kama kasurgumin a kan babur unguwar kwarkwaron Manu a yankin Basawa dake Tudun Wadan Zaria. 


Jaridar Premium Hausa ta rawaito cewa ”Yan sanda dake fatorol a unguwar Kwarkwaron Manu, Basawa ne suka kama shi. Ko da suka hango su bisa babur din da babu lamba a jiki sai suka tsaida su. Wanda aka goyo ya sauka ya arce kafin ‘yan sandan su ankare. Daga nan ne fa aka damke matukin.


” Bayan an gudanar da bincike sai aka gano cewa wannan matukin kasurgumin dan bindiga ne kuma dillalin saida wa ‘yan bindiga bindigogi da harsasai. An kama buhu lode da harsasai har sama da 300 da aka kirga su, sannan da bindiga kirar AK47 4,da layu da guraye.


Jama'a na bayyana ra'ayin su akan wannan nasarar da jami'an tsaro suka samu akan kama wannan dan bindiga. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post