Jiragen Yakin sojin Najeriya sun yi luguden wuta kan yan ta'adda a Borno sun kashe fiye da 100


A wani hari da rundunar sojin Najeriya suka kai a maboyar Boko Haram dake jihar Borno sun yi luguden wuta inda suka kashe mayakan fiye da 100. 


Edward Gabwek wanda shine kakakin rundunar ya ce sun samu bayanan sirri kan maboyar yan Boko Haram hakan yasa aka yi umarnin kai hari da jiragen Yaki a maboyar su. 


"A harin farko mayakan da suka tsallake rijiya da baya sun koma wurin domin daukar gawarwakin ’yan uwansu da jiragen yakin suka kashe, wanda hakan ya kara ba wa jiragen damar aika sama da mutum 100 a cikinsu lahira, wasu gommai kuma suka samu munanan raunuka.” cewar Edward Gabwek


Shafin Aminiya ya rawaito cewa bayan kai harin an samu mutuwar wasu daga cikin manyan kwamandojin Boko Haram wanda suka hada da Khalid Tukur, Maimusari, da kuma Bakura Jega. 


Samun bayanan sirri ya taimakawa jami'an tsaro dakile yunkurin da mayakan ke Shirin kaiwa a yayin bukukuwan kirsimeti da kuma babban zaben da za'a yi na shekarar 2023.


Hare-haren da rundunar ta kai a baya-bayan nan a maboyar su sun gurgunta harkokin ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas, cewar Edward Gabwek. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post