A cigaba da nuna murna da zagayowar bikin ranar haihuwarta jaruma Rahama Sadau ta cigaba da wallafa hotunanta masu kayatarwa.
Mutane dai na ta bayyana ra'ayoyinsu kan irin hotunan da jarumar ke wallafawa inda wasu ke bayyana ra'ayinsu akan rashin dacewar yin hakan, wasu kuwa na ganin hakan ba wani abu bane.
Rahama Sadau tun tsawon lokaci tana wallafa hotuna wadanda ke jawo tafka yin muhawara a Kafar soshiyal midiya.