Ikilima Yusuf jaruma dake fitowa a cikin shirin kwana casain mai dogon zango ta yi bikin cikar ta shekaru 26 a duniya.
Jarumar ta yi bikin walimar ranar zagayowar haihuwarta a ranar Asabar wanda kawayenta da yan Kannywood suka halarci taron.
Shafin Film Magazine ya rawaito cewa anyi walimar ne a Kano kuma maata yan Kannywood da suka halarci walimar akwai Safiya Adam, Rashida Adamu Abdullahi da sauransu.
Bayan kammala cin abinci anyi kide-kide da raye-raye tare da cahsewa. Bayan hakan jarumar ta yi jawabin godiya musamman ga wadanda suka halarci walimar.