Halartar mabiya mazhabar Shia bikin Kirsimeti ya bar baya da kura, inda a ranar Lahadi aka hangi wasu daga cikin malamai daga mazhabar sun halarci wata majami’a a Zariya don taya kiristoci murna tare da basu kyautuka.
Aminiya ta rawaito cewa malaman sun kai ziyarar ne lokacin ibada a majami’ar Ekelisiyar (EYN) dake unguwar Samaru a Zariya domin su taya su murna da kuma kara fuskantar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban a Najeriya.
Farfesa Isa Mshelgaru da yake jawabinsa yayin kai ziyara a majami’ar ya ce dalilin kai ziyarar shine don su taya kiristoci murnar ranar haihuwar Yesu Almasihu, domin musulunci ya ce idan wani bai zama dan uwanka na addini ba, zai zama dan uwanka na mutuntaka.
Duk da addininmu ya banbanta mu da su duk mutanene. Mun yi shawarar zuwa wannan waje saboda yaune ranar da aka haifi Yesu Almasihu wacce duk duniya ake yin wannan bikin hakan yasa muka zo don mu nuna musu kauna.
Irin wannan alaka tana da muhimmanci sosai domin Musulmai suna daukar kiristoci a matsayin yan uwan su duba da La'akari da halin da Najeriya take ciki, cewar Farfesa Isa.
A karshe ya yi Kira ga yan Najeriya da su kara hada kai ba tare da nuna bambancin addini yare, kabila ko siyasa ba domin hakan ne kawai zai iya ceto kasar daga halin da take ciki.