Lokacin da ake jin yunwa kuma aka samu aka ci abinci akwai bukatar a samu a huta domin abinci ya gama zama a jiki. Sai dai ba kowane yake yin hakan ba.
Akwai wadanda da Zarar sun kammala cin abinci za su koma su ci gaba da gudanar da harkokin su wanda Kuma hakan babban illa ne ga lafiyar jiki.
Hakan yasa masana kiwon lafiyar abinci suka bayyana wasu abubuwa da mutum zai yi da kuma Kauracewa yi da zarar ya kammala cin abinci.
A cikin wannan video za ku ji wasu abubuwa 3 da mutum zai guji yinsu da zarar an gama cin abinci domin kare lafiyar jiki da inganta lafiya.