Bidiyon ƙaramin jaririn ya ɗauki hankali kuma ya sami ra'ayin mutum miliyan 29 bayan an wallafa shi a ranar 5 ga Disamba a shafin "Kitchen Kun Suda."
Abin mamaki, a ƙoƙarinsa na ciyar da kansa, Yaron ya ƙare da yin wanka da taliyar a jikin sa. A cikin bidiyon Kuna iya ganin dogayen taliyar na rataye a kansa, kafadunsa, cikinsa, fuskarsa da kowane bangare na jikinsa.
A gabansa akwai faranti na taliyar sai dai ya juye ta a dukkan jikinsa fiye da farantin. Da alama yaron ya ƙi barin ciyar da kansa saboda har yanzu yana da wasu taliyar a hannunsa. Shima bakinsa na motsi yana taunawa, ma'ana wani abincin ya shiga bakinsa.