Rahotanni sun ce an gano buhunan rubabbun takardun kudi na naira a barikin ‘yan sanda a Jihar Benue.
Wani faifan bidiyo da aka yada a yanar gizo ya nuna buhunan kudi na miliyoyin Naira da suka lalace da aka ce an gano su a barikin 'yan sanda na Wadata dake jihar Benue.
Ana iya jin wata muryar mutane a cikin faifan bidiyon suna cewa, "Kalli kudi a Wadace amma sun rube, duba kudi, duba inda aka boye kudi har aka bari suka lalace.