Auren miji mai mata shine abu mafi kyau domin yana zuwa da grabasa biyu, ga Miji ga 'yar'uwa


Wata budurwa da ta wallafa wani rubutu a shafinta na twitter ya jawo cece-kuce inda ta bayyana cewa auren miji mai mata shine mafi dacewa don akwai garabasa saboda ga miji ga kuma yar uwa.


Ba kasafai dai aka saba jin mata suna irin wannan kalaman ba, saboda babu wata mace da take da burin ta auri namiji wanda yake da mata musamman ga budurwar da ba ta taba yin aure ba.


Wannan yasa akai ta tabka muharawa tun bayan rubutun da budurwar ta wallafa. Inda masu yin tsokaci suka dinga yaba mata ciki har da tsohon sanatan kaduna Shehu Sani wanda ya ce batun ki "gaskiya ne".

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post