Hotunan wasu ango da amarya da suke ta yawo a shafukan sada zumunta sun jawo cece-Kuce inda a cikin hotunan amaryar ta bata rai babu walwala a fuskarta.
Hakan ya jawo ana ta tafka muhawara inda wasu ke ganin akwai alamun rashin kauna daga fuskar Amaryar.