An kama wata budurwa da ake zargin tana kokarin yin sata da ciki na karya a wani shahararren kantin sayar da kayayyaki a Middelburg, Mpumalanga, Afirka ta Kudu.
Lamarin da ya baiwa kowa mamaki. An tattaro cewa masu gadi ne suka tsayar da ita a bakin kofa yayin da take kokarin fita.
Da aka bincika ta, sai aka gano cewa haƙiƙa ba ta da ciki amma ta ƙirƙiri wani abu mai kama da ciki na jabu da nufin ɓoye kayan da ta sata a cikin kantin.
Yayin da bincike yai nisa sai aka tabbatar da cikin na karya ne. Yanzu haka dai an mika budurwar ga jami'an yan sanda don cigaba da gudanar da bincike.