Labaran Kannywood
Yanzu-Yanzu: Kakar Darakta Falalu A Dorayi Ta Kwanta Dama
Tuesday, November 15, 2022
0
INNA lillahi wa inna ilaihir raji'un! Allah ya yi wa kakar jarumi kuma darakta a masana'antar Kannywood, Falalu A. ÆŠorayi, rasuwa. Hajiya Amina, wadda ake kira Nene ko Yakumbo ko Yadikko, ta rasu a yau a Kano.
Marigayiyar ta rasu ta na da shekara 110 a duniya. A sanarwar rasuwar da Falalu ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa za a yi jana'izar ta ranar Talata da Æ™arfe 12 na rana a Gidan MaÆ™era da ke unguwar Ja’en ÆŠorayi.
Da fatan Allah ya yi mata rahama, Allah ya kyautata makwancin ta, amin.
Previous article
Next article
Leave Comments
Post a Comment