'Yan sanda sun ceto wata yarinya 'yar shekara 17 da ake zargi An daure ta a tirken Akuya a Filato


Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta ceto wata yarinya ‘yar shekara 17 da ta yi fama da rashin cin abinci mai gina jiki, wadda aka yi zargin innarta ta kulle a cikin tirken akuya sama da mako guda a garin Rikkos da ke karamar hukumar Jos ta Arewa. 


Wata makwabciyarta ta sanar da hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa a Jos bayan an gayyaci ‘yan sanda, lamarin da ya kai ga ceto ta. 


Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya tattaro cewa goggon na son cin zarafi da kuma kashe yarinyar, wacce marainiya ce. 


Ko’odinetar hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa a Filato, Misis Grace Pam, ta tabbatar da ceto yarinyar a wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a 18 ga watan Nuwamba, 2022.


 “Hukumar ta samu labari daga wani mai korafin da ba a bayyana sunansa ba cewa ’yar uwarta ce ta kulle yarinyar a barandar wani gida,” inji ta.


 “Tana zaune da kakarta kafin ta zo gidan inna saboda kakar ba ta da lafiya kuma ba za ta iya ci gaba da kula da ita ba.


 “Mai karar ya yi zargin cewa goggon ta yi tafiyar kusan mako guda ta bar yarinyar babu ci babu sha. 


“Bincike ya nuna cewa lallai yarinyar tana fama da rashin abinci mai gina jiki kuma akwai tabo a hannunta, wuyanta da sauran sassan jikinta.


 “Alamomin sun samo asali ne daga dukan da aka yi mata ba kakkautawa daga wajen innarta, an kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda inda aka dauki bayanin goggon bayan ta dawo daga tafiyar ta.


 “Yarinyar an samar mata da matsuguni na wucin gadi har sai ta warke, mun kuma gano cewa yarinyar marainiya ba'a barinta fita ko ina, amma an kulle ta a gida ba a ba ta abinci ba, wani abokin aikinmu ne ya kai ta asibiti domin tabbatar da kulawar da ta dace,'' ta kara da cewa.


 Pam ya koka da yadda ake samun karuwar cin zarafin kananan yara a cikin ’yan kwanaki da suka gabata, yana mai jaddada cewa “yayin da muke magana, akwai wata yarinya ‘yar shekara tara da aka kashe, wadda ta zo ta zauna tare da kawarta watanni biyu da suka wuce. 


“Dole ne mu kubutar da ita a ranar Alhamis daga hannun kawarta, ta yi mata dukan tsiya, amma alhamdulillahi, ba ta samu makanta ba, amma ta samu rauni a idonta, inda muka kai ta asibiti ranar Juma’a sakamakon mummunan duka da aka yi mata. "


 “Lokacin da ma’aikatanmu suka je wurin, an kulle ta a wani gidan kiwon dabbobi inda goggo ke ajiye awakinta. Yarinyar tana fatan komawa wurin danginta

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post