src='https://pagead2.googlesyndication.com/pagead/js/adsbygoogle.js?client='/> Yadda sojin Najeriya suka yi luguden wuta a maboyar yan ta’adda a Kaduna - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Yadda sojin Najeriya suka yi luguden wuta a maboyar yan ta’adda a Kaduna


Rundunar sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe yan bindiga a maboyar su dake dazukan Kaduna tare da kwato makamai masu yawa a yayin kai harin. 


Anyi nasarar kashe mayakan ne a wani sumame da dakarun soji suka kai musu a maboyarsu inda aka dinga yi musu lugudan wuta ta jiragen saman yaki. 


A hirar da yai da BBC Mr Samuel Aruwan ya ce an kai farmakin ne a maboyar yan bindigar dake Chikun, Igabi, Kajuru da Giwa. Wanda a yayin kai harin an Kashe yan bindigar da dama tare da kwace makamansu. 


Kawo yanzu dai babu wata sanarwa na adadin yan bindigar da aka kashe da adadin makaman da aka kwato, sai dai an yi nasarar kubutar da mutane da dama da aka yi garkuwa dasu. 

Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel