Yadda Jami'an Soji Suka Lalata Maboyar Yan Bindiga Tare Da Ceto Wasu Da Aka Yi Garkuwa Dasu


Rahotanni daga Jihar Kaduna na cewa jami'an tsaro sun ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a sansanonin masu garkuwa da mutane.


Shafin BBC Hausa ya rawaito cewa, Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ne ya tabbatar da hakan inda ya ce an gano gawarwakin mutum biyu waɗanda aka yi garkuwa da su.


Dakarun Operation Forest Sanity ne suka kai samame a ƙananan hukumomin Chikun da Kachia da Kajuru inda suka lalata sansanoni da dama na ƴan bindiga.


Gwamnatin Kaduna ta bayyana cewa tun da farko dakarun na Operation Forest Sanity ne suka yi musayar wuta da ƴan bindiga a kusa da Kwanti da ke Ƙaramar Hukumar Chikun.


Bayan ƴan bindigan sun afka cikin daji, sai suka bar babura waɗanda daga baya dakarun suka ɗauko.


A baya-bayannan dai jami'an Soji suna samun nasara sosai a yakin da suke yi da yan bindiga a Jihar Kaduna, wanda hakan ke nuna za'a iya kawo karshen ayyukan 'yan ta’adda. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post