Yadda Aka kubutar Da Wata Mata Da Mijinta Ya Daure Ba Ci Ba Sha Tsawon Watanni


Wata mata mai suna Sadiya Salihu mai shekara 33 ta shaki iskar yanci bayan da maigidanta ya daure ta a cikin gida tsawon watanni. Sai dai yanzu tana cikin wani mawuyacin hali na tsananin rashin lafiya. 


Aminiya ta rawaito cewa Mijinta Ibrahim Yunusa wanda shine ake zargin ya tsare matarsa tsawon watanni cikin mawuyacin hali wanda yanzu ya jefata cikin matsananciyar rashin lafiya wanda yanzu haka take kwance a asibitin kudi a unguwar Sheka dake Kano. 


Sadiya dai yar asalin jihar Kano ce wacce ta koma zama a garin Nguru na jihar Yobe bayan da ta yi aure a watan Afrilun 2010, wanda a yanzu haka ta haifi 'ya'ya hudu da mijin nata. Shi kuma mijin nata Ibrahim Yunusa dan asalin jihar Borno ne wanda zama ya dawo dashi jihar Yobe. 


A tattaunawar da Aminiya ta yi da mahafiyar Sadiya ta ce bayan da taje garin na Nguru domin duba yarta sai ta sameta cikin mawuyacin rashin lafiya da azzalumin mijinta ya jefa ta. 


Na dade ina yin mugayen mafarki akan 'yar tawa kuma duk lokacin da na Kira mijinta kan ya hadani da ita za mu yi magana sai yace ai baya gida ko kuma ya hadani da yara su kuma su ce ai barci take yi. Hakan yasa na shirya na tafi garin ba tare da na fadawa kowa ba wanda ba don naje ba da tuni ta rasa ranta. 


Da na tambaya ance mijin nata koko kawai yake bata da gasashen naman hasbiya, hakan yasa ta karfi na dauko 'yata na tawo da ita gida. Hakan yasa dole aka cire cikin da take dauke dashi na wata 11 saboda halin da take ciki. 


Sunce suna zargin mijin da yin amfani da ita don yin tsafi wanda yasa yake hanata abinci sai koko da gasashen nama kawai don ta mutu. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post