Wata mata da har yanzu ba ta samu miji ta yi aure ba, Atieno Massey, ta yi kalaman yabo ga matar da take mata aiki a gida yayin da ta saki Bidiyon matar tare da ɗan karamin ɗanta.
Massey ta nuna jin daɗinta game da yadda 'yar aiki ke kaunar ɗanta kuma ta roki Allah ya albarkaci matar saboda halaccin da take yi mata.
A wani Bidiyo da ta saki a shafin TikTok, Massey ta bayyana cewa ta shiga ɗaki kenan sai ta hangi yar aiki da kuma ƙaramin yaron suna kwance a gado suna bacci tare.
Da take ba da amsar wasu sakonni, Massey ta ce zancen gaskiya har yanzun bata yi aure ba kuma tana rayuwa ne daga ita sai ɗanta sai kuma wannan yar aiki.
A kalamanta tace: "Gayu ina godiya da yadda kuka faɗi ra'ayoyinku amma a zahirin gaskiya ban kai ga yin aure ba, ina zaune ne da wannan yar aiki kamar yar uwata saboda tana ƙaunar yaron da na haifa."