Ba kasafai aka fiye jin ko ganin maza na kashe kansu ba a dalilin soyayyar da suke yiwa mace ba. Galibi dai an fi samun hakan a bangaren mata.
Sai dai a wannan labarin wani matashin dalibi ne dake karatu a kwalejin fasaha ta tarayya ta Oko dake a Jihar Anambra ya hallaka Kansa saboda yarinyar da yakeso taki amincewa da soyayyar sa.
Shafin BBC ya rawaito cewa dalibin ya yanke hukuncin kashe kansa bayan da budurwar da yake matuƙar kauna ta ce masa ba ta son sa yaje ya nemi wata.