Wata Kotun Shari'ar Musulunci dake zamanta a unguwar Magajin Gari a Jihar Kaduna, a ranar Litinin ta umarci wata matar aure mai suna Maryam Ɗahiru, kan ta dawo da sadakin kudi dubu dari da kayan lefe da ta karɓa daga tsohon mijinta, Salihu Yakubu.
A yayin da yake yanke hukunci, Alƙalin Kotun mai shari'a Malam Rilwanu Kyaudai, ya tabbatar da raba auren tsakanin mutanen biyu ta hanyar Khul'i (Wato yarjejeniyar saki ta fahimta).
Jaridar Legit Hausa ta rawaito cewa Alkalin ya bawa Maryam Dahiru umarnin ta dawo da kayan da bata taɓa sakawa ba kaɗai kuma ita da ta kawo ƙara tana da umarnin Kotu ta koma ta kwashe kayanta daga gidan tsohon mijinta."
Abinda ya jawo mutuwar auren shine, Tun farko dai, Maryam ta hannun Lauyanta Murtala Gyallesu ta shigar da ƙarar mijinta ranar 12 ga watan Oktoba, 2022 tana mai rokon Kotu ta rabasu ta hanyar Khul'i.
Ta shaida wa Kotun cewa bata sha'awar ci gaba da zaman auren kuma a shirye take ta biya kudin sadaƙin da aka biya a kanta domin samun takardar saki.
A na shi ɓangaren Salihu Yakubu ta bakin lauyansa M. M. Ɗahiru, ya faɗa wa Alkalin cewa har yanzun yana ƙaunar matarsa kuma bashi da niyyar sakinta.
Ya kuma roki Kotun ta umarci tsohuwar matarsa ta dawo masa da akwatunan da ya cika da kayayyaki, wanda ya bata a matsayin kyauta lokacin aurensu.