Mun Kusa Yin Aure Ni Da Nura Mustapha Waye Kafin Rasuwarsa - Inji Hajara Izzar So


Aisha Babandi wacce aka fi sani da sunan Hajara a cikin shirin "Izzar So" mai dogon zango, a wata tattaunawa da aka yi da ita ta bayyana cewa ta shiga mawuyacin hali tun bayan rasuwar Darakta Nura Mustapha Waye. 


Ta bayyanawa Freedom Radio cewa kafin rasuwar Nura sun shaku da juna sosai wanda har ya Kai ga maganar aure. 


Ta ce tana matukar Kaunarsa domin shine mutumin da ya taimakeni a har aka sanni a masana'antar Kannywood kasancewar na taso a gaban yar uwar mahaifiyata don ba ni da uwa da uba, cewar ta. 


Ko mutuwar iyaye na ba ta taba ni kamar ta Nura ba domin na taso bansan iyayena ba bansan dadin su ba. Soyayya da shakuwa ta yi karfi sosai a tsakanin mu kafin ya rasu. 


Ta bayyana rasuwar Nura a matsayin abinda ba za ta taba mantawa dashi ba. Sai dai ta yi addu'a Allah ya jiƙan marigayin, ya mayar mata da makamancin sa.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post