Mayakan Boko Haram Sun Yi Wa Wasu Mata Yankan Rago Kan Zargin Su Da Maita


Ana zargin kungiyar 'yan ta'adan Boko Haram da kashe wasu mata ta hanyar yi musu yankan rago a yankin Gwoza dake Jihar Borno wanda suke zargin matan da kashe kurwar 'ya'yan kwamandojin mayakan. 


Aminiya ta rawaito cewa tun a satin da ya gabata ne mayakan na Boko Haram suka tsare mata su 40 a kauyen Gwoza wanda kwamandan su Ali Guyile  ya basu umarnin tsare su. 


Wata mata da ta samu kubuta daga hannun mayakan ta shaidawa manema labarai cewa lamarin ya faru ne bayan mutuwar wasu 'ya'yan kwamandan Boko Haram inda suka zargi matan da lashewa 'ya'yan nasu kurwa. 


Hakan yasa suke zargin matan kauyen da maita wanda kwamandan ya bayar da umarnin a duba duk wani gida da ake zargin akwai mayya a cikinsa kafin daga bisani ya yiwa wasu daga cikin su yankan rago. 


Sai da suka kashe mata 14 a ranar Alhamis kan zargin su da maita inji matar kamar yadda ta shiada a wata hira da Radio Faransa sukai da ita bayan ta kubuta daga hannun mayakan na Boko Haram. 


Ta kara da cewa mayakan sun yi ikirain cigaba da zakulo dukkan wasu matan da da suke da hannun kan mutuwar 'ya'yan nasu, a cewar matar. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post