HOTUNAN: Yadda 'Yan Kannywood Suka Yi Cincirindo A Bikin Halima Atete


Yadda 'yan Kannywood maza da mata suka yi cincirindo wajen halartar bikin jaruma Halima Atete ya nuna cewa jarumar ta kowa ce a masana'antar kuma ta zauna da kowa lafiya. 


Domin kuwa manyan jarumai maza da mata da manyan mawaka daga masana'antar Kannywood suka yi tattaki har zuwa birnin Maiduguri don taya Halima murnar bikin ta. 


A irin wannan yanayin da ake ciki na fargarbar tsaro da jihar Borno ke fama dashi hakan bai hana abokan sana'arta daga sassa daban-daban sun je wajen bikin ba. Hakan ne yake nuna cewa jarumar ta yi zaman lafiya da kowa.











Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post