Gaskiya Na Gaji Da Zama Ni Kadai Ina Bukatar Miji, Cewar Wata Matashiya


Wata matashiyar budurwa ta koka Kan zaman da take yi na rashin abokin rayuwa. Wanda ta bayyana hakan na matukar damunta. Ta ce a satin da ya gabata taje bikin saka ranar auren wata aminiyarta wanda hakan ya Kara sakata a cikin damuwa. 


A wajen shagalin matan da suke da miji duk sunje da mazajensu, mu Kuma da ba mu da miji haka muka zauna gefe guda abin haushi. Wannan dalilin yasa na kara son kasancewa da namiji a tare dani. 


Abinda zai baka mamaki yanzu sai ka samu 'yan mata wanda shekarunsu ya haura 30 Kuma suna da sana'a da masu aikin yi da suke samun kudi, suke da gidaje da motocin hawa na kansu amma Kuma sai ka same su ba su da miji, cewar matashiyar. 


Matashiyar ta fito a shafinta na dandalin sada zumunta inda ta bayyana cewa tana neman miji saboda ta gaji da zama babu aure, duk wanda ya shirya yin aure yai mata magana. 


Shin Menene ra'ayinku game da wannan batun matashiya? 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post