Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun a ranar Juma’a, 25 ga watan Nuwamba ta kama wani dan luwadi dan shekara 36 mai suna Sikiru Ajibola bisa zarginsa da yin lalata da wani yaro dan shekara 5 a unguwar Ogijo a jihar Ogun.
An kama wanda ake zargin ne biyo bayan rahoton da shugaban CDA na Olorunwa Arogbeja Ogijo ya gabatar a hedikwatar Ogijo, wanda ya bada rahoto cewa daya daga cikin al’ummar yankin ya sanar da shi cewa wanda ake zargin yana da masaniya kan wani yaro dan shekara 5 da yake yin mu'amala dashi ba bisa ka’ida ba, wanda hakan yai sanadin mutuwar yaron.
Bayan rahoton, DPO reshen Ogijo, CSP Enatufe Omoh, ya yi gaggawar tura jami’an bincikensa zuwa inda lamarin ya faru inda nan take aka cafke wanda ake zargin.
Shafin Linda Ikeji, ya rawaito cewa wanda ake zargin a lokacin da ake yi masa tambayoyi, ya amsa laifin cewa shi dan luwadi ne kuma a lokacin da yake yin amfani da yaron ya mutu nan take.
Ya kara da cewa ya yi gaggawar tona wani kabari mara zurfi a wani daji da ke kusa, inda ya yi gaggawar binne yaron. Ya kuma kai ‘yan sanda inda ya binne gawar yaron.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abimbola Oyeyemi, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Lanre Bankole, ya bayar da umarnin mika lamarin ga sashen binciken kisan gilla na sashin binciken manyan laifuka na jihar domin ci gaba da bincike da kuma tabbatar da hukunci ga mai laifin.