Zafafan Sunayen Soyayya Guda Uku Da Za Ku Riƙa Kiran Abin Ƙaunar Ku Da Su


Haduwar farko a tsakanin masoya yakan iya kasancewa wani bakon abu, domin yana da wuya a lokacin ka gane irin kalaman da ya dace ka furta na soyayya. 


Dukanmu muna da nau'in sunaye waɗanda muke amfani da su wajen kiran abin kaunar mu. Wasu suna kiran masoyin su da "Honey, Baby, Sweetheart, Masoyi, ko Masoyiya kodai wasu sunayen na dabam. Fitowa da suna da za ku furtawa abin kaunar ku salo ne na ƙara shakuwa.


Ga Wasu Daga Cikin Sunaye Irin Na Soyayya Da Masoya Ke Furtawa Abin Ƙaunar Su


1. Kyakkyawawa: Lokacin da kake gayawa abar Ƙaunar ka cewa ita din mai kyau ce. Yana sa ta ji daɗi da amincewa a cikin zuciyar ta cewa koyaushe tana yin imani da kai, kuma hakika kana son ta. Za ta yi maka komai.


2. Baby: Wannan shi ne wani classic domin furta wannan sunan sai wanda ya cancanta ake iya kira da wannan sunan, domin na musamman ne. Idan ka kira ta da irin wannan suna, yana sa ta manta da duk wata matsala da ta shiga kuma ta ji za ta iya fadamaka komai nata. A irin wannan yanayi, ba za ta boye maka komai ba.


3. Darling: Lokacin da kuka sami kanku kuna jin kunya kamar yadda kuka yi lokacin da kuka fara haduwa. Kamar yadda muka sani, manta ranar farko da kuka hadu da masoyinku na daya daga cikin manyan ranaku da ba zaku iya mantawa da su ba. Tabbas ko da yaushe za ku tuna saboda irin sa'ar wannan ranar. 


Wasu lokuta wasu ma suna yin rubutu don kada su manta. A wannan yanayin, kiranta da suna darling zai sa taji kamar babu wata mace kamar ita. Kuma yana sa ta jin daɗin yin magana da kai a koyaushe kuma ta rayu cikin farin ciki tare da yanayin halin da ake ciki.


Waɗannan su ne sauƙaƙan sunaye guda uku mafi yawan ƙara soyayya don kiran abokiyar zaman ku waɗanda nake fatan za ta so shi sosai. Ku gwada yin hakan kuma na yi muku alkawarin duk wacce kuke kira da irin waɗannan sunayen za ta kara son ku sosai.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

3 Comments

Previous Post Next Post