Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun harbe dalibar makarantar AAU da ta kammala karatun aikin Likitanci a kan hanyarta ta koma gida Abuja.
Dalibar mai suna Celestina ta kammala karatunta na digiri a bangaren aikin Likitanci a jami'ar Ambrose Ali dake Ekpoma.
Kwanaki 13 da shigar da ita Cibiyar Nazarin Lafiya ta Najeriya, Celestina na kan hanyar komawa Abuja, inda take zaune, a lokacin da wasu ‘yan bindiga da ba a tantance Ko suwaye ba suka harbe ta har lahira.
Celestina kafin mutuwarta ta taba zama mataimakiyar shugabar kungiyar likitocin Katolika da daliban hakora (FECAMDS) Najeriya sau biyu.
Labarin rasuwarta ya girgiza wadanda suka santa inda suka shiga shafin Facebook suna jimamin mutuwarta.