Yadda 'yan bindiga suka sace wasu dalibai a Kan hanyarsu ta komawa makaranta bayan dage yajin aiki


Wasu guggun yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace daliban jami'ar Nsukka dake Jihar Enugu akan hanyarsu ta komawa makarantar bayan dawowa daga hutun yajin aiki. 


Shafin BBC ya rawaito cewa lamarin ya faru ne a karamar Hukumar Igbo-Etiti na Jihar ta Enugu a yammacin ranar Lahadi. Sai dai babu wani rahoto akan adadin daliban da 'yan bindigar suka sace. 


Rahotan na cewa 'yan bindigar na yawan kai hari a hanyar suna yin garkuwa da matafiya. Tun bayan harin da suka kai a ranar Asabar sun cigaba da kai farmaki a hanyar har zuwa Talata. 


Ana zargin mahukanta da kasa daukar mataki akan ayyukan 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane a sassan jihohin Najeriya.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post