Wasu mutane da ake zargin yan daba ne sun Kai hari ga masu zagayen maulidi a Jihar Naija inda suka hallaka mutum daya tare da raunata wasu da dama kamar yadda Aminiya ta rawaito.
Lamarin dai ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 4:00 na yamma a garin Chanchaga kusa da Masallacin Juma’a na Chanchaga dake a Minna babban birnin jihar ta Naija.
Ana tsaka da gudanar da zagayen na Mauludi sai aka hangi 'yan daba dauke da manyan makamai suka far wa masu zagayen maulidi suka fara yin sara.
DSP Wasiu Abiodun wanda shine kakakin rundunar yan sandan jihar ya tabbar da Kai harin inda yace mutum daya ya mutu yayin da mutane hudu suka samu mummunan raunuka wanda aka kaisu asibitin kwararru domin kula da lafiyarsu.