Yadda Aka Kulle Wani Dattijo Tsirara A Wani Ɗaki Har Tsawon Shekaru 20


Dattijo mai kimanin shekaru 60 ya shaƙi iskar ƴanci bayan shafe shekaru 20 a rufe cikin wani ɗaki dake layin Benin a tsakiyar garin Kaduna.


Jaridar Tribune ta rawaito cewa a ranar Laraba ne ne dai wasu masu aikin duba gari suka yi nasarar ganin mutumin sannan suka fitar dashi daga wajen da aka ajiye shi na tsawon wannan shekaru 20.


Mai magana da yawun ƴan sandan jihar DSP Mohammed Jalige ya bayyana cewa sun samu rahoton daga wajen jami'an duba gari game da yadda suka gano dattijon inda kuma ba tare da bata lokaci ba muka tura jami'an mu wajen.


Jalinge ya ƙara da cewa sun gano mutumin ne tsirara babu kaya jikinsa kulle a cikin wani ɗaki a wani gida dake kan hanyar Bayajjida dake cikin garin Kaduna. Sai dai mazauna gidan sun tsere kafin isowar hukumar ƴan sanda.


Sai dai ya tabbatar da cewa za su gudanar da bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin.


A baya-bayan nan dai ana yawan samun faruwar irin hakan inda ake samun iyaye ko dangi suna daure ƴan uwansu a daki na tsawon lokaci. Sai dai wasu na ganin cewa kamata yai duk wanda aka samu da aikata irin hakan a dinga ɗaukar matakai masu tsauri a Kansu.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post