A safiyar Talata ne a ka wayi gari da tsayawar Manhajar whatsapp a Najeriya da sauran wasu sassan kasashen duniya har da Britania.
Masu yin amfani da manhajar fiye da dubu 10 ne suka bayyana daina turawa da karbar sako tun wajen karfe 8 na safiyar Talata.
Sai dai wasu rahotanni daga shafin BBC sun tabbatar da cewa ba ko inane aka samu matsalar ba akwai wasu kasashen da ba su fuskanci hakan ba duk da basu bayyana sunayen kasashen ba.
Sama da mutane biliyan biyu ne dai ke yin amfani da manhajar ta whatsapp a fadin duniya, wanda suke gudanar da harkokin kasuwancin su.
Ko a watannin baya ma an taba samun irin wannan matsalar ta tsayawar kafofin sada zumunta wanda sai da akai kusan awa biyu kafin ya dawo.