Wani Sabon Aure Ya Mutu Bayan Da Tsohon Saurayi Ya Turawa Angon Hotunan Amarya Tsirara


Wani sabon aure da Ko tarewa ba'a yi ba yazo karshe, bayan da tsohon saurayin amarya ya turawa da angon wasu hotunan amaryar tsirara wanda hakan yasa angon ya rubuta takardar saki nan take. 


Sai dai da ake tambayar amaryar dalilin faruwar hakan ta bayyana cewa ta yi soyayya da tsohon saurayin sai dai daga baya ta fuskanci ba abokin zama bane hakan yasa ta rabu dashi, kamar yadda shafin Lisa ya rawaito. 


Tace tasan ta yi Kuskure a baya amma kuma tun da ta samu mijin aure ta tuba ta daina domin tana so ta sake sabuwar rayuwa, amma duk da haka tsohon saurayin bai daina bibiyar ta ba, cewar ta. 


Ta Kara da cewa iyayen ta sun fito mata da miji shi kuma tsohon saurayinta bai shirya yin auren ba kuma ba yi zai yi ba hakan yasa na mayar da hankalina wajen wanda iyayena suka zaba min, cewar amaryar. 


Anasa bangaren angon ya ce ana cikin shagalin biki aka turo masa da wani sako cikin envelope cewa ka duba abinda ke cikin memory kuma kasani cewa matar da za ka aura mutuniyar banza ce. 


Hakan yasa yai saurin saka memory a cikin wayar sa domin ganin abinda ke faruwa, wanda kuma yana budewa ya samu hotunanta na lalata ba tare da kaya a jikinta ba. 


Lamarin bai yi min dadi ba domin na gano cewa tsohon saurayinta ne ya turomin da hotunan, hakan yasa nai gaggawar kawo karshen shagalin bikin da ake gudanarwa a lokacin, cewar angon. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post