Fitaccen jarumi a masana'antar Kannywood Adamu Abdullahi wanda ake yiwa lakabi da Adam Zango ya bayyana yadda ya shiga sana'ar harkar finafinan Hausa.
Adam Zango a wata tattaunawa da aka yi dashi da gidan "Radio Freedom Kano" ya bayyana cewa rashin kuɗin da zai cigaba da karatu ne yasa ya yanke shawarar shiga sana'ar haƙar ma'adanai wacce kuma daga bisani ya koma sana'ar Film.
Zango ya ƙara da cewa tun tasowarsa shi mutum ne mai son neman na kansa, kuma ya shigo sana'ar tun a shekarar 2003 wanda kuma har zuwa wanan lokaci ake damawa dashi a masana'antar ta Kannywood.
Yanzu haka dai Adam Zango na ɗaya daga cikin manyan jarumai a masana'antar Kannywood wanda suka ɗauki tsawon lokaci taurarawarsu na haskawa.