Yahanasu Sani daya ce daga cikin jaruman Kannywood mata wanda suka daɗe a masana'antar suna bayar da gudummawa tsawon shekaru. Domin kuwa ta ce ta shafe tsawon shekaru 20 tana cikin masana'antar.
Abinda yaja hankalin Yahansu shiga masana'antar Kannywood akwai kawarata Aisha Kiyarda dani ita ce ta jawo Yahansu zuwa Kannywood. Wanda aka kaita wajen Baba Ɗan Azumi Chediyar Ƴan Gurasa.
Yahansu ta bayyana cewa Ɗan Azumi Baba shine wanda ya fara sakata a film kuma shine darakta din ta na farko. Ta fara fitowa a wani film mai suna 'SAUDATU'. Tun daga wannan lokacin har zuwa yanzu Hajiya Yahansu ta yi finafinai da dama.
Daga baya an daina ganin Hajiya Yahansu a cikin finafinan Kannywood wanda aka bayyana ta yi aure, sai dai kuma daga baya ta dawo ta cigaba da yin finafinai.
Wani shiri mai dogon Zango da ake yinsa na Kwana Casa'in da tashar Arewa 24 take daukar nauyi har da Hajiya Yahansu a ciki wanda take taka muhimmiyar rawa sosai a cikin shirin.
Yahanasu ta yi aure har da 'ya'ya huɗu Fatima, Sadiq, Abduljabar sai dai guda ɗaya daga cikinsu Hindatu ta rasu.
Hajiya Yahansu ta bayyana irin nasarorin da ta samu tun bayan shigar ta harkar film, domin kuwa har kujera ta rike ta S'A, kuma suna zaune da kowa lafiya a cikin masana'antar ta Kannywood.
Baya ga harkar Finafinai Hajiya Yahansu tana yin kasuwanci, sannan kuma ita ƴar siyasa ce. Ta bayyana Ɗanwake a matsayin abincin da tafi so.