Najeriya dai ta samu 'yancin kanta a shekarar 1/10/1960 daga hannun mulkin mallaka da turawan Ingila suka yi mata. Tun daga wannan lokacin ne ake gudanar da bukukuwa na murnar samun 'yanci a fadin ƙasar.
Sai dai duk da wannan tsawon shekaru da aka shafe na shekaru 62 da samun 'yancin kan wasu na ganin babu wani sauyi na cigaba da kasar ta samu.
Sai dai fa har yanzu kasar nan na neman mafita bisa halin data shiga, na gaza kaiwa matakin da ake ta mafarki tsawon shekaru nan. Ga wasu daga cikin nazarin da mukai a cigaban da kasar ta samu tun daga 1960 zuwa yanzu.
Fannin ilimi, duk da irin cigaban da ake ganin an samu, amma idan ka kwatanta na Najeriya da sauran kasashe sai kaga batun fa cigaba na Jama'a da gina ajujuwa da kawata makarantun aka samu, amma madarar ilimi, sai dai nan gaba domin har yanzu ba a manta da batun yajin aiki a Najeriya ba.
Haka fanin Tattalin arziki domin tsofaffi sunce gwara lokacin turawan domin akwai saukin rayuwa sama da yanzu, haka kuma kudadenmu suna da daraja, amma a yanzu kullum masana sai sun kawo wani tsari dan a gwada karshe dai talakawa ne suke shan gwale gwale.
Fannin wutar Lantarki za a iya cewa shima gwara jiya da yau domin cikin shekara daya an dauke wuta sau babau adadi a kasa baki daya, Dan haka maganar Lantarki ita ma gwara lokocin turawan duk da cewa Jama'a babu yawa amma akwai tsari mai kyau.
Bangaren Tsaro babbar magana, domin shima an samu koma baya idan aka kwatanta da shekarar 1960 zuwa yau 2022/Oct/1 batun tsaro sai ayi wani sabon zubi, sabo da laifukan da a lokacin baya ba a sansu ba yanzu sun mamaye Najeriya, sai dai yanzu Najeriya tana da sojoji sama da shekarun baya duk da haka suna bukatar kayan aiki domin kara musu karfi.
A bangaren siyasa a Jamhuriyar ta farko da ta biyu da uku har zuwa yau an samu cigaba domin an zare sojoji daga harkokinta bare ayi maganar juyin Mulki, kuma talakawa da dama sun zama Shugabanni a kowane matakin, sai dai har yanzu akwai sauran rina a kaba sabo da mafi yawan 'Yan siyasa na yanzu ba jagoranci nagarine agaban su illa su tara abin Duniya sababin lokacin baya shekaru 62 da suka gabata.
Kazalika fannin lafiya an samu manyan asibitoci sama da lokacin baya an kuma samar da kwararrun likitoci sama da lokacin 1960, Kuma Jama'a yanzu sun yarda suje asibiti sababin shekarun baya, amma duk da haka akwai bukatar daura damarar samar da magunguna da inganta aikin da samar da Karin Ma'aikata.
A yanzu Najeriya tana da mutane sama da miliyan dari biyu sababin shekaru sittin da biyu kuma ta samu arzikin ma'adanai sama da lokacin baya, sannan ta samu hanyoyi da harkokin sufuri duk da cewa basu da yawa Kuma hanyoyin sun farfashe, Amma dai sun Fi na da , wadan da babu kwalta.
sai dai Yan Najeriya na fatan zaben dake tafe duk wanda ya zama Shugaban Najeriya zai dubi halin da kasar ke ciki domin kawo gyara.