Sheikh Aminu Daurawa Yaja Kunnen Masu Yada Hotunan Amaryarsa A Soshiyal Midiya



Shehin Malami Aminu Daurawa ya yi kira tare da jan kunnen masu yaɗa hotunan sabuwar amaryarsa a shafukan soshiyal midiya wacce ta ciyo gasar Alqur'ani maigirma ta ƙasa baki ɗaya. 


Amaryar mai suna Haulat Aminu Ishaq Ana sa ran cewa malamin zai angwance da hafizar a makon gobe. Wanda Yace baiji daɗin yadda wasu mutane ke yaɗa hotunanta a shafukan sada zumunta na zamani ba. 


Hakan yasa amaryar fashewa da kuka bayan samun labarin yadda hotunanta suke ta yawo a duniya. Bai kamata mutane su dinga yaɗa hotunan ba don ba abar talla bace, cewar malamin. 


Abinda ake bukata shine saurin auren irin wannan ƴan mata hafizai bawai waɗanda suka shahara a bikin gasar kyau na mis Naija ba. Sannan yaja hankalin waɗanda suke yayaɗa hotunan da su daina. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post