Wani saurayi dake zuwa zance wajan budurwar sa ya jiwa mahaifin budurwar rauni bayan ya umarce shi yadaina kaiwa dare idan yazo zance.
Mahaifin ya umarci saurayin cewa idan har dagaske ne zai auri 'yar tasa ya turo mahaifansa ayi magana a daura aure.
Jin haushin maganar da mahaifin budurwar yai yasa saurayin ya dauki mummunan mataki akansa inda yai masa dukan tsiya har ya ji masa mummunan rauni a jikinsa.
Lamarin dai ya faru ne a garin dan Hassan da ke yankin Karamar Hukumar Kura ta jihar Kano. Sai dai yanzu jami'an tsaro sun yi nasarar kame matashin domin gurfanar dashi a gaban kotu.
allah ya shirya mana matasan mu
ReplyDeleteAllah ya bashi lafiya,inda ace anabin shari'a tun farko karfin ya fara zuwa zance zai turo iyayen sa a nema mishi izini sabo da haka yazamo aya ga iyayen da suka bari maza na zuwa fira wurin ya'yansu ba tare da sun turo iyayen su ba
ReplyDeleteHassana
ReplyDeleteHassana
ReplyDelete