Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama wani matashi dan shekara 39 mai suna Mfon Jeremiah mazaunin FIRRO Estate dake garin Adesan, Mowe bisa laifin yiwa diyarsa mai shekaru 13 ciki (wacce a sakaya sunanta).
An kama wanda ake zargin ne biyo bayan rahoton da uwar yarinyar ta kai hedikwatar Mowe, inda ta bayyana cewa ‘yarta na dauke da juna biyu, kuma da ta tambayi ‘yar, ta sanar da ita cewa mahaifinta ne ya kwana da ita.
Sai dai bayan da hukumar 'yan sanda suka karbi rahoton sun tura yarinyar asibiti don yin gwaji, wanda kuma likita ya tabbatar da cewa yarinyar tana dauke da ciki wata hudu.
Bayan rahoton, DPO Mowe, SP Folake Afeniforo, ya yi umarni ga jami'an 'yan sanda da su yi gaggawar yin cikakken bincike a gidan ake zargin inda nan take aka kama shi.
A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifin da ke tuhumar sa na yiwa ‘yarsa cikin, amma ya yi ikirarin cewa baya cikin hayyacinsa a lokacin da ya aikata hakan. Ya sanar da ’yan sanda cewa yana mafarkin yin jima'i tare da matarsa da suka rabu da shi na tsawon wani lokaci sai kawai ya gano cewa ’yarsa ce yake saduwa da ita.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abimbola Oyeyemi, ya ce kwamishinan ‘yan sandan, CP Lanre Bankole, ya bayar da umarnin mika wanda ake zargin zuwa sashin yaki da safarar bil’adama da aikin kananan yara na sashen binciken manyan laifuka na jihar domin ci gaba da bincike. da kuma yiwuwar gurfanar da shi gaban kotu.