Mutumin Da Yafi Kowa Kazanta A Duniya Ya Mutu Yana Da Shekaru 94


Rahotanni sun bayyana cewa mutumin da ya fi kowa kazanta a fadin duniya ya rasu yana da shekara 94 da haihuwa. 


Amou Haji wanda dan kasar Iran ne ya rasu ne a ranar Talata 25 ga Oktoba 2022 bayan ya kwashe shekaru 67 bai yi wanka ba.


Kafin rasuwarsa, abincin da yake ci sun hada da rubabben nama da matattun dabbobi. Yana matukar jin dadin cin bushiya da shan tabarsa ta koko kuma yake rage tashin kansa ta hanyar konarsa da wuta kamar yadda rahotanni suka bayyana.


Hajji ya yi imanin cewa ruwa da sabulu za su sa shi rashin lafiya wanda shi ya sa ya kwashe tsawon wadannan shekaru ba tare da yin wanka ba.





Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post