Wani matashi dan Najeriya ya sayar da kodar sa domin ya sayi sabuwar wayar iPhone da aka saki ta sama da Naira miliyan 1.4. Yaron wanda dalibi ne a Jami’ar Fatakwal (UNIPORT), an ce ya sayi wayar iPhone 14 bayan ya sayar da Kodarsa. An tattaro cewa ya sayawa budurwar wayar mai tsadar gaske saboda tsananin son da yake yi mata.
Wani hoto da ke zagayawa a shafukan sada zumunta ya nuna shi rike da wayar iPhone yayin da yake nuna cikinsa da filasta a gefen dama na kusa da inda aka cire Kodarsa.
Wani mai amfani da kafafen sada zumunta ya bayyana labarin, inda ya rubuta cewa; "Dalibin Uniport ya sayar da KODARSA don siyan IPHONE 14 ga budurwarsa, ya ce ya yi hakan ne domin yana son yarinyar"
Labarin dai ya jawo tafka muhawara sosai a kafafen sada zumunta inda mutane ke ta bayyana ra'ayoyinsu. Wasu na ganin cewa dalibin yayi wauta da yawa, wasu kuwa na ganin ai soyayya ce ta ke jawo hakan.