Matasa A Jihar Lagos Sun Ƙone Wasu Mutane Biyu Ƙurmus A Dalilin Satar Kuɗi Wajen Mai POS


Wasu fusatattun matasa sun ƙone wasu mutane biyu da ake zargin su da sacewa mai yin POS kuɗi a jihar Lagos.


SP Benjamin Hundeyin kakakin rundunar ƴan sandan Jihar Lagos ya tabbatar da faruwar hakan a shafinsa na twitter inda ya bayyana yadda fusatattun matasan dake unguwar Igando suka ƙone matasan su biyu ƙurmus.


Sai dai rundunar ƴan sanda ba ta samu labarin faruwar lamarin ba sai bayan da matasan suka ɗauki doka a hannu. Ko bayan da rundunar ta isa wajen jama'ar da suka yi aika-aikar sun tsere.


Sai dai Hundeyin ya ce tuni suka fara gudanar da bincike akan lamarin don gano waɗanda suke da hannu a cikin wannan aika-aikar.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post