Tun a ranar Litinin ne dai wani labari ya karade shafukan sada zumunta kan cewa wani Malamin jami'a Bisi Olawuyi na jami'ar gwamnatin tarayya dake Ibadan ya rabawa dalibansa su 10 $100 Kowanen su.
Sai dai a yammacin ranar Talata ne malamin ya fito a shafinsa na Twitter ya bayyana labarin da mara tushe da asali, domin shi baisan wannan magnar ba a sakon da ya wallafa Kamar haka.
"Hankalina ya karkata ga wani sako na twitter da ke yawo cewa na baiwa dalibai 10 $100 kowanne. Wannan ba gaskiya bane ta kowace hanya. Da fatan za a yi watsi da wannan labari mara tushe. Na gode."