Bisi Olawuyi wani malamin Jami'a dake koyarwa a Jami'ar Tarayya ta Ibadan ya bayar da kyautar dala dari ga dalibansa da suka halarci aji a ranar farko tun bayan dawowa daga yajin akin ASUU na tsawon wata takwas.
Malamin yayi hakan ne duba da yadda duk dalibai basu halarci darasin ba sai guda 10 kadai. Hakan yasa yai amfani da wannan damar ya rabawa kowane daga cikinsu dala dari wanda yakai kimanin kusan dubu 73,000 a canjin kudin Najeriya.
Shafin LindaIkeji itace ta rawaito labarin inda ta bayyana cewa wani daga cikin daliban da suka samu wannan kyautar ya tabbatar musu da hakan. Inda yace su kansu daliban sun yi mamaki sosai da samun kyautar.